Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita na sa’o’i 16 a wasu ƙananan hukumomi 10 kan matsalar tsaro a jihar. Sanarwar da sakataren gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki daga yau, ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026, kuma za ta kasance […]
Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wani ƙuduri da ke neman dakatar da duk wani sabon matakin soja kan Iran ba tare da sahalewar Majalisar Dokoki ba. Sanatoci 50 ne suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ƙudurin, yayin da 48 suka nuna adawa da shi. Sanatocin jam’iyyar Republican, Bill Cassidy na Louisiana, Susan Collins ta Maine, […]
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci jami’an rundunar da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da rikon amana, tare da kauce wa karɓar cin hanci da rashawa. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Area Command Wudil, inda ya gana da […]
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Jagoran Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Guzape a Abuja ranar Talata. Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam, da Shehu Wada Sagagi, Nasiru Garo da sauran manyan jagororin NDC. […]
Rundunar ƴan sandan jihar Kadun,a ta gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare mai lamba huɗu bisa zarginsu da hannu a kisan wata malamar Islamiyya mai suna Ummulkhairi a yankin Mararrabar Jos da ke jihar Kaduna. Ana tuhumar mutanen da laifin haɗa baki da tayar da tarzoma da ɓarnata dukiyar jama’a da ta ƴan […]
Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya a Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce ta ceto mutane sama da 47, akasarinsu mata da yara, daga hannun ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno. Jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Maiduguri. […]
Kotun tarayya da ke sauraron shari’ar zargin sauraron wayoyi ba bisa ka’ida ba da ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta ƙi amincewa da buƙatar da aka gabatar na neman sassauta sharuɗɗan belinsa. Alkalin kotun, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta bayyana cewa sharuɗɗan beli masu tsauri da aka kafa tun farko za […]
Cutar Ebola ta kama sama da mutane dubu daya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, yayin da barkewar cutar ta bazu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na uku, sannan ta yi sanadin mutuwar wata yarinya yar kimanin watanni 18. Gwamnatin Kongo ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 254. Yaduwar cutar cikin sauri […]
Tawagar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura zuwa Najeriya don gudanar da bincike a game da zargin kisa da yin garkuwa da mutane da kuma tilasta wa wasu mutanen barin muhallansu saboda dalilai na addini, ta ce waɗannan zarge-zarge ba gaskiya ba ne. Jagorar tawagar Farfesa Nazila Ghanea, ita ce ta sanar da hakan bayan […]