Labarai

Gawuna ya koma ADC a hukumance, ya yi rajista a matakin mazaba.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya koma jam’iyyar ADC a hukumance, inda ya kammala rajista tare da karɓar katin zama ɗan jam’iyya a mazabarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar. Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gawuna ya je yin rajistar tare da jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon ɗan takarar shugaban […]

Read more

Ƴan majalisar wakilai 8 na Kano sun fice daga NNPP zuwa APC

Ƴan Majalisar Wakilai takwas daga Jihar Kano sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar NPP zuwa jam’iyyar APC, lamarin da ya ƙara girgiza siyasar jihar. Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya sheƙar a hukumance yayin zaman majalisar a yau Talata, bayan karanta wasiƙun da ‘yan majalisar suka aike wa zauren. A cikin […]

Read more

El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa. An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa […]

Read more

Sojoji sun ceto mutane 157 da ISWAP ta sace a Borno

Sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai sun ceto fararen hula aƙalla 157 da ’yan ta’addan Boko Haram suka sace a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun ce a ranar 30 ga Maris da misalin ƙarfe 2:50 na rana aka kai wa dakarun bataliyar sojoji ta musamman ta 135 da aka tura […]

Read more

Komawar Kwankwaso ADC barazana ce ga APC

Mai fashin baƙi akan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Ibrahim Sadauki Kabara, ya bayyana cewa komawar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jam’iyar ADC babbar barazana ce ga jam’iyyar APC a Kano dama ƙasa baki ɗaya. Komawar Kwankwaso, wanda shi ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, […]

Read more

Kwankwaso ya koma jam’iyyar ADC tare da magoya bayansa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP. An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shuwagabannin jam’iyyar da dimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa. Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa […]

Read more

PDP tsagin Wike ta zaɓi sabbin shugabanninta

Jam’iyyar PDP tsagin Mininstan Abuja, Nyesom Wike ta zaɓi Abdulrahman Mohammed a matsayin sabon shugabanta na ƙasa yayin da Samuel Anyanwu ya samu matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Mohammed da Anyanwu sun samu kujerunsu ta hanyar masalaha, tare da sauran mambobin kwamitocin jam’iyyar ta ƙasa guda 19 a babban taron jam’iyyar na shekarar 2026 da […]

Read more

Gawuna ya ajiye muƙamin da Tinubu ya ba shi

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya. Sanarwar da tsohon mataimakin gwamnan ya fitar ta nuna cewa ajiye aikin zai fara ne daga gobe Talata, 31 ga Maris, 2026. A […]

Read more