Ƴan sanda sun kama wata mata da zargin satar kaya na sama da miliyan 10 a Katsina.
Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta kama wata mata mai shekaru 27, Hadiza Ibrahim, bisa zargin satar kayayyaki daga wani shago da darajarsu ta kai naira miliyan 10.1. Mai magana da yawun rundunar, DSP Aliyu Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an kama matar […]