Rusau: Gwamnatin Kano Ta Rushe Wani Gini Dake Daula Otel
Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya cigaba da abin da ya yi alkawari na karbe filaye gwamnati da aka yi gine-gine a kan su. A daren Lahadin nan, labari ya zo daga gidan rediyon Freedom cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ruguza gini da aka yi a otel da ake kira da Daula.