Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce sun yi nasarar kwato filaye na triliyoyin Nairori
A jiya Juma’ar nan ne aka ga Hukumar Tsara birane ta jahar kano KNUPDA ta shafa Jan fenti ga Dogayen gine-ginen da aka yi tare da ba su wa’adin kwance gine-ginen bisa hujjar cewa an yi su akan Badala.