An haramta sana’ar bola-jari a Gombe
Gwamnatin Gombe ta haramta sana’ar bola jari a duk faɗin jihar, bisa abin da ya kira barazanar tsaro da kuma zargin sana’ar da ƙarfafa ayyukan laifi. An yanke wannan shawara ne a wani taron Majalisar Tsaro na musamman da gwamnatin jihar ta gudanar tare da manyan jami’an tsaro, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, domin […]