CBN ya ƙara yawan kuɗin da ake iya cirewa a mako

Babban Bankin Najeriya (CBN) a jiya ya soke iyaka kan adadin kuɗin da ake iya ajiyewa a banki tare da ƙara kuɗin da ake iya cirewa daga naira 100,00 zuwa naira 500,000 a kowane mako.

Wannan canji ya fito ne a cikin wata sanarwa da bankin ya aika wa dukkan bankuna wacce Dr. Rita Sike, Daraktar Sashen Tsare-Tsaren Kuɗi da Dokoki, ta sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce daga 1 ga watan Janairu, 2026, za a yi amfani da waɗannan sabbin dokokin kuɗi a duk fadin Najeriya.

“An soke iyaka kan addadin kuɗin aka ake iya ajiyewa a banki da kuma kudin da ake biya idan an wuce iyaka. Haka kuma an ƙara kuɗin da ake iya cirewa zuwa naira 500,000 ga mutum ɗaya kuma naira miliyan 5 ga kamfanoni. Idan aka wuce waɗannan iyakokin, za a cire kuɗin tara.

A bangaren injin cire kuɗi kuma, iyakar kuɗin da mutum zai iya cirewa zai kasance N100,000 a rana kuma N850,000 a kowane mako.

A cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi da magance matsalolin tsaro da kuma daƙile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda