Chadi ta rufe kan iyakarta da Sudan

Ƙasar Chadi ta rufe kan iyakarta da Sudan har zuwa wani lokaci.

Sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin dakatar da kutsen da ƙungiyoyi da ke ɗauke da makamai na Sudan ke yi a ƙasar.

A cikin sanarwar, ministan harkokin sadarwa na Chadi, ya ce ya na son ya daƙile duk wani haɗarin bazuwar rikicin zuwa ƙasarsa

A ranar Asabar da ta gabata an samu ɓarkewar faɗa a garin Al- Tina da ke kan iyaka, tsakanin mayaƙan RSF da wasu mayaƙa da ke goyon bayan sojojin Sudan.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya