Nijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyu

Jamhuriyar Nijar ta amince da kundin ayyukan Ƙungiyar Kasashen Sahel (AES) na shekara ta biyu wadda ta haɗa da Mali da Burkina Faso, kafin taron ministoci da za a gudanar a Ouagadougou daga 24 zuwa 26 ga watan Fabrairu, kamar yadda jaridar gwamnati ta ANP ta ruwaito a ranar 21 ga Fabrairu.

Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine ya gana da ministoci da mambobin kwamitin ƙasa na AES a ranar 21 ga Fabrairu domin daidaita matsayi kafin taron yankin.

Mataimakiyar Shugabar kwamitin, Bayard Mariama Gamatie, ta ce Burkina Faso ta raba wani kundin aiki, wanda Nijar ta gyara bisa ginshiƙai uku da suka haɗa da tsaro da diflomasiyya, ci gaban ƙasa, da tsaro da kare iyaka.

“An amince da kundin gaba ɗaya, dangane da shawarwarin gyare-gyaren Nijar,” in ji Gamatie.

Rahoton ya nuna cewa ministocin Nijar sun duba kundin sun kuma yi gyare-gyare da sake fasalta wasu abubuwa, sannan sun bayar da shawarwari don taron ƙwararru da zai biyo baya.

An kafa AES a shekarar 2023, bayan da ƙasashen uku suka janye daga Ƙungiyar ECOWAS, domin tsara manufofi na tsaro da diflomasiyya, da ci gaban ƙasa tsakanin ƙasashen Sahel.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC