Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 7 A jihar Zamfara

Rahotanni na nuna cewa cutar kwalara ta barke a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara inda zuwa yanzu ta hallaka aƙalla mutum bakwai a ƙananan hukumomin Gumi da Bukkuyum.

Hukumomin sun ce kusan mutum 200 cutar ta kwantar a asibitin kananan hukumomin biyu, tare da gargadin cewa adadin na iya karuwa.

Hon Sulaiman Abubakar Gumi wanda shi ne danmajalisar tarayya da ke wakiltar Gumi/Bukkuyum kuma shugaban kwamitin hukumar raya yankin arewa maso yammaci a majalisar wakilai, ta Najeriya ya shaida wa manema labarai cewa tun daga ranar 10 ga watan nan na Agusta, 2025 matsalar ta fara inda yanzu take ta karuwa.

Ya ce zuwa yanzu a Bukkuyum kadai an kwantar da mutum wajen 157, tare da fargabar yawan zai iya karuwa da kuma fargabar rasa wasu mutanen a sakamakon cutar.

Danmajalisar ya ce a Birnin Waje inda ba a kai rahoton bullar cutar ba ma da wuri har an yi mace-mace, inda aka rasa mutum bakwai zuwa yanzu.

Hon Gumi ya ce, a karamar hukumarsa ta Gumi ma a Unguwar Gamji wajen mutum 24 aka kwantar a asibiti.

Ya kara da cewa a kasar gaftu akwai wata kungiya da ba ta gwamnati ba – kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya , MSF, suna taimakawa.

Hon Abubakar ya yi gargadin cewa muddin ba a dauki matakin gaggawa ba abin zai iya zama annoba.

Bayanai dai sun nuna cewa kusan duk shekara akan fuskanci barkewar wannan cuta ta kwalara a jihar ta Zamfara a daidai irin wannan lokaci na damuna, wanda hakan ya sa ake ganin rashin daukar wani kwakkwaran mataki na hana hakan.

Dangane da hakan ne sai danmajalisar ya ce a wannan karon matsalar ta taso ne a sanadiyyar ‘yan gudun hijira da ke zaune a kasar Bukkuyum.

”Suna zaune ne a makaranta a tsakiyar gari, to matsalar da nake ji, masansu ta rufta saboda ruwan sama, sai ya zama cewa babu wajen zuwa makewayi sai nan cikin gari magudanar ruwa inda suke tsugunawa cikin dare su biya bukatarsu, ina ganin daga nan ne matsalar ta fara yaduwa,” in ji shi.

Dangane da tallafin gwamnati, danmajalisar ya ce har dai zuwa lokacin da yake yi wa BBC bayani babu wani tallafi da gwamnati ta kai sai dai wanda mutanen gari da kuma su suke yi.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto