Yan Sanda A Kano Sun Kama Barayin Motoci

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu satar motoci ne tare da gano motoci uku da aka sata a wurare daban-daban.

A sanarwa da rundunar ta fitar ranar Talata, , ta bayyana cewa ta cafke mutanen biyu tare da wata motar Siena Bus a karamar hukumar Wudil bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa.

Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike, sannan za a mika motoci ga masu su.

Kwamishinan ‘Yan Sandan CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewar jami’an rundunar tare da gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen bayar da bayanan sirri.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.