Home » Dillallan Ƙwaya Sun Shiga Komar NDLEA A Faɗin Ƙasar Nan

Dillallan Ƙwaya Sun Shiga Komar NDLEA A Faɗin Ƙasar Nan

by Halima Djimrao
0 comment

A taronta na manema labarai na wannan makon Hukumar yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi, NDLEA, ta ce jami’anta sun kama lodin tabar wiwi nau’in skunk a ɓoye a cikin gwangwanayen tumatir da wasu ƙwayoyin kuma da aka cusa a cikin tsofaffin tufafi da niyyar kai wa Dubai.  A babban filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammad aka kama miyagun ababen sa mayen waɗanda  nauyinsu ya kai kilogra kusan 22.

Haka kuma jami’an Hukumar ta NDLEA sun kama wata tabar wiwi ƴar Canada mai nauyin giram 556 wadda aka .turo ta daga ƙasar Canada zuwa wani mutum mai suna Tunji Adebayo  da ke Ikorodu a jihar Legas. Da jami’ai suka je gidansa sun kama ƙaninsa wanda ya tura karɓar saƙon.

A halin da ake ciki kuma a makon da ya gabata jami’an Hukumar NDLEA sun yi dirar mikiya a tungar Abdul Rauf wani ƙasurgumin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo, a unguwar Akala, a Mushin da ke jihar Legas inda suka samu tabar wiwi ƴar Ghana mai nauyin kilogra dubu ɗaya da ɗari da ɗaya, kuma suka kama mutane uku, sai dai shi gogan ya tsere.

A wannan makon ma a jihar Kogi jami’an Hukumar sun kama wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Agada Emmanuel yana ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogra kusan 78 akan babban titin da ya ratsa  Okene da Lokoja zuwa Abuja, haka kuma an kama ƙwayoyin haɗiya iri-iri har guda dubu 369 da ɗari 9 da 80, kuma bincike ya kai ga kama wani mutum mai suna Kabiru Ahmad Abdullahi a garin Gwambe wanda shi ne ya mallaki lodin ƙwayoyin.

Kakakin Hukumar Femi Babafemi ne ya yi wannan bayani a cikin wata sanarwar da ya fitar a ƙarshen mako.

Kuma yace jami’an Hukumar sun kama wani mutum mai suna Asana Oluwagbenga Leke mai shekaru 39 yana ɗauke da ababen fashewa ƙirar gida, guda 399 akan hanyar Mokwa zuwa Jebba.

Mutumin yace an ba shi su ne a wata tashar motar Ibadan  aka ce da shi ya kai wa wani a Kaduna, kamar yadda Femi Babafemi ya faɗa a cikin sanarwar. Kuma tuni an miƙa mutumin da ababen fashewar ga hukumomin soji a jahar Neja.

A Jihar Ogun ma wani mai suna Yinka Azeez mazaunin Sabo Lafenwa a Abeokuta ya shiga hannun hukumar bayan wani binciken da aka gudanar game da wata tabar wiwi mai nauyin kilogra 41 da aka kama a wurin wani mai suna Titilayo Adetayo a wani titin Sagamu.

Sannan kuma jami’an NDLEA sun kama Muhammad Aliyu mai shekaru 38, da Abdullahi Zakariya ɗan shekara 40 suna ɗauke da tabar wiwi nau’in skunk mai nauyin kilogra kusan 427, an kama su ne bi da bi akan hanyar Zariya zuwa Kano da kuma unguwar Hayen Arewa, a Hotoro a jihar Kano.  

A jihar Imo an kama Onyeka Uzor ɗan shekara 25 a Idemili yana ɗauke da kilogra 65 na tabar wiwi da taramol, shi ma wani mai suna Destiny Irabor an kama shi da ƙwayoyin haɗiya kimanin kilogra 180 a cikin motarsa ƙirar Toyota Sienna. Akwai kuma Usim Orji wanda aka kama akan titin Aba zuwa Owerri ɗauke da ƙunshi 100 na tabar wiwi ƴar Canada mai nauyin kilogra 57.

A Kaduna an kama Ahmed Yusuf  da Rilwan Nura bayan wani binciken da aka gudanar game da ƙunshin tabar wiwi 100 masu nauyin kilogra 55 da aka kama kan hanyar Abuja.

Femi Babafemi yaci gaba da cewa a jihar Edo, jami’an hukumar sun kai farmaki cikin dajin Ekudo a ƙaramar hukumar Onwude inda suka lalata gonakin tabar wiwi masu faɗin kadada fiye da huɗu; Haka kuma jami’an sun afka wa gidan wani mai suna Amuodu Egwehide mai shekaru 40 a Iloje Okpuje a ƙaramar hukumar Owan ta yamma, inda suka samu tabar wiwi buhu 22 masu nauyin kilogra 261, a yayin da aka kama wata tsohuwa mai jikoki, Misis Eunice Egwehide mai shekaru 60 tana ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogra 17 ita ma a garin na  Iloje Okpuje.  

A jihar Yobe ma an kama tabar wiwi a hannun wani mai suna Gapchiya Modu mai shekaru 26 a Nguru, jihar Yobe. Haka kuma bayan dogon binciken da aka kwashe watanni biyu ana gudanarwa,  jami’an Hukumar NDLEA sun kama wani shugaban dillallan miyagun ƙwayoyi, Idoko Festus Ifesinachi mai shekaru 40, wanda aka alaƙanta da tabar wiwi ƴar Canada mai nauyin kilogra 77 a cikin wata kwantena a tashar jiragen ruwan Fatakwal. Daga bisani an kama shi a maɓoyarsa ta Legas kuma aka iza ƙeyarsa zuwa Fatakwal.

Kakakin Hukumar NDLEA Femi Babafemi ya ƙara da cewa bayan duka wannan ƙoƙari da suke yi na kama fataken miyagun ƙwayoyi, haka kuma suna ci gaba da yaƙi da shan ƙwaya ta hanyar faɗakarwa a makarantu da wuraren ibada, da gidajen sarakuna da kuma yankunan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar Najeriya.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?