Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci Yusuf Datti Baba-Ahmed, tsohon abokin takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaben 2023 tare da Peter Obi.
DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed ne a daren Juma’a bisa zargin ci gaba da bayyana ra’ayoyi da take ganin na iya tayar da hankali a Najeriya.
Wata majiyar tsaro ta ce DSS ta daɗe tana bibiyar kalaman Baba-Ahmed a kafafen yada labarai, musamman kan iƙirarin da ya yi na cewa akwai “rikicin kundin tsarin mulki” a Najeriya.
A cewar majiyar, “Kwanan nan Datti Baba-Ahmed ya bayyana a talabijin inda ya zargi kotuna da rundunar sojoji da rashin hana rantsar da Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, har ma ya yi nuni da cewa rantsar da Tinubu ta bai wa sojoji damar cin mutuncin mutane.
Ta ƙara da cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da tashin hankali a ƙasar, musamman a irin wannan yanayin siyasa da ake ciki.
- ADC ce kawai za ta ceto Najeriya – Atiku
- Kashim Shettima ya isa Bauchi halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi
Ta ce, “Abin damuwa ne ganin yadda irin wannan magana ta janyo rikice-rikice a wasu ƙasashe kamar Guinea-Bissau. Hukumar tsaro tana ɗaukar wannan da muhimmanci, ba don siyasa ba, sai don kare zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.”
A cewar majiyar, DSS ta yi wannan gayyata ne bisa ƙa’ida, saboda kalaman Datti Baba-Ahmed da suka yi kama da raina ƙoƙarin gwamnati wajen inganta tsaro a matsayin “wasa” na iya tayar da hankalin jama’a da kuma rage amincewa da hukumomin ƙasa.
Ta ce, “Wannan gayyatar ba hukunci ba ne, amma matakin kariya ne domin fayyace niyya, da manufar kalamansa a muhallinsu, da kuma hana fitowar labarai da za su iya haifar da rikici ba tare da an yi niyya ba.”
Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ba, haka kuma Datti Baba-Ahmed bai ce komai a hukumance kan gayyatar ba.