Duk Shugaban Da Bai Yi Aiki Ba Bai Kamata A Sake Zaɓarsa Ba — Jonathan

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba.

Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama.

Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana.

Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi, tsaro, kiwon lafiya, ayyukan yi.

A cewarsa, idan shugabanni suka gaza bayar da waɗannan abubuwa, jama’a kan rasa muradi da kyakkyawan fata.

Ya ƙara da cewa a inda ake gudanar da sahihin zaɓe, jama’a kan iya tsige shugaban da bai yi aiki , amma a ƙasashen Afirka, ’yan siyasa na amfani da maguɗin zaɓe don ci gaba da yin mulki ko da jama’a ba sa so.

Tsohon shugaban ya kuma yaba da yadda matasa ke ƙara shiga harkokin siyasa, sai dai ya jaddada cewa har yanzu suna buƙatar jagoranci da hikimar dattawa domin su yi nasara.

A wajen taron, Shugaban Ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo, da wasu shugabanni sun yi kira da a gaggauta gyara tsarin dimokuraɗiyya a Afirka.

Mahama ya ce dimokuraɗiyya ba za ta ɗore ba idan ‘yan Afirka ba su tsaya tsayin daka wajen kare ta da ɓunƙasa ta ba.

Ya ce dole a bunƙasa cibiyoyi, a kawo ci gaba, a tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da kare ’yancin ’yan jarida.

Obasanjo, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce yadda ake tafiyar da dimokuraɗiyya a Afirka a yanzu ba za ta ɗore ba, dole sai an yi wa tsarin gyara.

Sauran mahalarta taron kamar Shugaban Hukumar ECOWAS, Doktq Omar Touray, da Bishop Matthew Hassan Kukah na Katolika a Sakkwato, sun jaddada cewa dimokuraɗiyya a Afirka bai kamata ta tsaya kan zaɓe kawai ba, sai an haɗa da gaskiya da riƙon amana.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda