Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da inganta tsarin koyar da Alkur’ani a jihar, ya yi kafaɗa da kafaɗa da tsarin neman ilimi a zamani.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin rufe gasar karatun Alkur’ani ta jihar karo na 40, da aka gudanar a Dakin Taro na Sir Ahmadu Bello da ke Dutse.
Ya bayyana matasan da ke haddace Alkur’ani a jihar a matsayin “babbar ni’ima” ga al’umma, inda ya yi nuni da muhimmancin ilimin Alkur’ani wajen gyara hali da saukaka rayuwa.
Gwamna Umar Namadi ya buƙaci mahalarta gasar da su yi rayuwa da koyarwar Alkur’ani.
“Kasancewar waɗannan matasa da suka haddace Alkur’ani a cikinmu babbar ni’ima ce. Muna ganin amfanin wannan gasa ta karatun Alkur’ani da ake gudanarwa. Idan mutum ya samu ilimin addini, musamman na Alkur’ani, komai na rayuwa zai zo masa sauki,” in ji shi.
“Saboda haka, muna gode wa Allah da wannan rahama da Ya yi mana na bamu matasa masu baiwar haddace Alkur’ani.”
- Gawar Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Ta Iso Najeriya Daga Masar
- Ana Zargin Yan Sanda Da Halaka limami Ta Hanyar Duka A Kano
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa ilimin Alkur’ani ta hanyar Hukumar Tsangaya, wacce aka kafa domin hada ilimin Alkur’ani da tsarin karatun zamani da yi masa kasafin kudi na musamman.
Haka kuma, ya bayyana cewa za a tallafa wa daliban da suka fi kwarewa domin ci gaba da karatunsu, ko dai a bangaren ilimin addini ko kuma fannin zamani kamar injiniyanci da likitanci.
Ya yaba wa Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar Jigawa, Hukumar Tsangaya, da Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi saboda kokarin da suke yi wajen bunkasa ilimin Alkur’ani.
A bana (2025), gasar ta kunshi maza da mata a fannoni daban-daban da suka hada da karatun hizibi biyu, goma, talatin da kuma sittin na Alkur’ani mai girma.