Gwamnati Za Ta Sayar Da Gidaje 753 Da Aka Kwato A Hunnun Godwin Emefiele

Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na sayar da gidaje guda 753 da ta ƙwato daga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, waɗanda suke cikin kadarorin da Hukumar EFCC ta ƙwato daga hannun masu almundahana da kuɗin ƙasar.

Ministan gidaje na Najeriya ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata a lokacin da yake karɓar takardun gidajen daga hannun EFCC, kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Salisu Haiba ya fitar, ya ce, “ma’aikatar gidaje ta karɓa gidaje 753 da suke Abuja waɗanda Hukumar EFCC ta ƙwato daga tsohon babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.”

Ministan ma’aikatar, Ahmed Dangiwa, ya yaba wa ƙoƙarin Hukumar EFCC ɗin wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda