Yan Sanda Sun Kama Tare Da Harbe Masu Garkuwa Da Mutane A Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zargi da laifin garkuwa da mutane

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

SP Kiyawa, ya ce ana zargin mutanen da laifin yin garkuwa da wata mata mazauniyar karamar hukumar Minjibir inda suka kai ta jihar Jigawa don neman kudin fansa.

Bayan samun labarin ne aka tura dakarun yan sanda, inda suka yi arangama da wadanda ake zargin har suka harbe wasu daga cikinsu sannan suka kama sauran .

Haka zalika an kwato makamai, a hannunsu, kuma an kubutar da matar ba tare da an biya kudin fansa ba.

Post masu alaƙa

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.