Gwamnatin Najeriya za ta rage kashi 20% na magungunan da ake shigo da su kasar nan

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage shigo da magunguna cikin ƙasar daga kashi 60 zuwa kashi 40 cikin 100 domin bunkasa harkar sarrafa magunguna a cikin gida.

Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkar lafiya, Salma Anas-Ibrahim ce ta bayyana hakan a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya domin karfafa dabarun hadin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya a Abuja.

A cewarta, wannan wani ɓangare ne na burin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya gaba da nufin cike giɓin da ake samu a fannin kula da lafiya na ƙasar.

Sauran fannonin da sabuwar gwamnatin za ta fi bai wa fifiko sun haɗar da haɓaka damar samun ayyukan kula da lafiya ga kowa da kowa da shigar da al’umma cikin shirin inshorar lafiya na ƙasa da aƙalla kashi 40% don tabbatar da ganin duk ‘yan Najeriya ciki har da rukunin al’umma masu ƙaramin ƙarfi.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr