Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe

Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

Wani makusancin Farfesa Pantami da BBC ta zanta da shi ya ce tawagar lauyoyin ɗantakarar na PDP na nazarin hukuncin.

Kotun ta buƙaci jam’iyyar PDP ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani domin tabbatar da wanda zai yi wa jam’iyyar takara

A watan Yuni ne PDP ta bai wa Pantami tikitin takarar gwamnan Gombe bayan da ya gaza samu tikikin jam’iyyar APC.

Post masu alaƙa

Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau – Shettima

Kotu Ta Soke Tikitin Takarar Farfesa Pantami

Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka