Hukumar kashe gobara ta Nijeriya, ta ce har yanzu tana gudanar da bincike kan abunda ya janyo tashin gobara sau biyu a kasuwar Singa dake jihar Kano.
Shugaban hukumar na ƙasa, Dakta Olumode Samuel Adeyemi, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a birnin Kano.Dakta Olumode Samuel, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya bayar da umarnin turo ƙwararru da za su bincika lamarin da kuma bayar da shawarwari don magance matsalar tashin gobara a kasuwannin ƙasar.
Shugaban hukumar kashe gobarar na tarayya, Dakta Olumode Samuel, ya bayyana cewa, ministan harkokin cikin gida Dr. Olubinmi Tunji-ojo, ya bayar da umarnin bude ofishin hukumar a cikin kasuwar Singa da gudanar da bincike don kare sake samun matsalar a nan gaba.
Shugaban hukumar ta tarayya reshen jihar Kano, Kazeem Sholadoye, wanda yayi magana a madadin shugaban na ƙasa, ya ce bababbar matsalar da suke fuskanta, ita ce rashin haɗin kan jama’a da kuma cushewar kasuwar.Haka zalika ya ce, ana yawan samun tashin gobara ta dalilin haɗa wutar lantarki (wayarin)bisa rashin tsari da ingancin kayan aiki.haka kuma ya bayyna takaicin yadda wasu mutanen ke girke-girke a kasuwannin.
A ƙarshe hukumar ta ce an rasa rayuka, amma har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano gawarwakinsu waɗan da aka rasa ɗin, sakamakon rashin ganinsu da aka yi.Inda ake kyautata zaton suna cikin guraguzai a inda lamarin da ya faru.