Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ii ya ɓukaci jama’a su yafewa juna.

Mai martaba sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sunusi ii, ya buƙaci jama’a su kasance masu haɗin kai da yafewa juna, kan dukkan wata matsala ta rashin jituwa.

Dr. Muhammadu Sunusi ii, ya bayyana hakan yayin sanar da ganin jinjirin watan Azumin Ramadan na shekarar 2026.

Ya ce , an ga watan a masarautar Katsina da Daura da Guru da Shalai, kamar yadda shehun Bornon ya sanar da ganin watan, inda ranar laraba ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1447.

Ya kara da cewa bayan zama da malamai, a jihar Kano sun amince a ɗauki azumin , kuma jama’a su tsarke niyarsu domin wata ne da ake samun falala mai yawa.

Haka zalika ya yi kira ga mawadata su ci gaba da taimakawa marasa ƙarfi.

Mai martaba sarkin ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo ƙarshen satar waya, shan ƙwaya, garkuwa da mutane, fashi da makami, faɗan daba da sauransu.

A ƙarshen ya yi addu’ar Allah ya ci gada da bawa jihar Kano da Nijeriya zaman lafiya mai ɗorewa.

Post masu alaƙa

DSS ta kama waɗanda ake zargi da sace Farfesa A Nasarawa

An gurfanar da waɗanda ake zargi da sace ɗaliban Oyo

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kwace kadarorin Godwin Emefiele