Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12 Tare Da Jikkata 5 A Kano

Mutane 12 ne suka rasu sakamakon hadarin mota daya auku da safiyyar yau juma’a a kauyen samawa dake karamar hukumar Garun Malam.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa dake nan Kano ya bayyana cewa hadarin ya rutsa da wata mota kirar DAF.

Yace motar tana dauke ne da kayayyaki dabam dabam na amfanin yau da kullum.

Haka kuma motar tana dauke da fasinjoji.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Labaran ya bayyana cewa mutane 19 ne hadarin ya rutsa dasu inda mutane 12 suka mutu nan take kuma an kai gawawwakin asibitin Nasarawa yayinda kuma sauran da sukaji ciwo ake kulawa dasu a asibitin Garin Kura.

Ya ce hadarin ya faru ne bayan da tirelar ta kwace daga hannun direban.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi