Jami’an DSS Sun Kama Mutane 5 Da Ake Zargin Sun Kashe Yarinya Bayan Sun Yi Garkuwa Da Ita A Kano

Hukumar tsaron fari ta DSS reshen jihar kano, ta samu nasarar kama wasu matasa biyar da ake zargi sun yi garkuwa da wata karamar yarinya mai suna Sakina Mamuda, yar shekaru 8 sannan suka halaka ta ta hanyar murde wuyanta tare da jefa gawarta cikin Rijiya.
Lamarin ya faru a unguwar Duhunbake ,dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barista Haruna Dederi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.
Dederi, ya ce wadanda ake zargin sun hada kai tare da aikata mummunan aikin, yin garkuwa da yarinyar tare da neman a biya su kudin fansa duk da haka suka kashe ta.Wadanda ake zargin sun hada da, Zailani Rabi’u, Hafizu Yusuf Muhd, Abubakar Abdulkarim watoDanyaro, Umar Lawan Abdullahi da kuma Amadu Salisu wato Amadi.

Kwamishinan shari’ar ya jinjinawa hukumar tsaron farin kayan kan nasarar da suka samu na kamo dukkan wadanda ake zargin cikin yan kwanaki kalilan.
Ya kuma ce gwamnan jihar Kano , Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya na mika sakon jaje ga iyayen yarinyar da al’ummar Garin Duhunbake da kuma karamar hukumar Gwarzo.
A Karshe ya ce gwamnatin jihar Kano ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma dukiyoyinsu don haka zata ci gaba da ba wa hukumomin tsaro hadin kai wajen gudanar da aiyukansu.

Post masu alaƙa

Da buƙatar samar da takin zamani ga manoman Najeriya – MDD

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kammala tantance masu neman shiga aikin ɗan sanda

Ƴan sanda sun tsaurara tsaro a cibiyoyin JAMB jihar a Jigawa