Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba Da Sarki Sanusi Sun Tafi Saudiyya

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, tare da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, sun tafi ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata.

Gwamnan ya jagoranci tafiyar ce domin halarta Sallar Jana’izar a Madina ne, bayan rasuwar hamshaƙin attajirin a birnin Dubai da ke ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ƙarshen mako.

Kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawaki tofa ne ya sanar da haka a safiyar Litinin.

A ranar Lahadi Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin Saudiyya sun amince da yin jana’iza da binne Alhaji Aminu,  Ɗantata a Madina, kamar yadda ya bar wasiyya.

Tuni tawagar manyan malaman Kano tare da Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar suka rika suka isa Madina domin halartar jana’izar.

Malaman sun haɗa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta Bashir Aliyu Alfurqan da Khalifa Limamin Masallacin Sanusi Ɗantata.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu