Home » Jihar Jigawa Ta Haɗa Guiwa Da Saudiyya Wurin Noma Dabino

Jihar Jigawa Ta Haɗa Guiwa Da Saudiyya Wurin Noma Dabino

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙulla ƙawance da kamfanonin samar da dabino na ƙasar Saudiyya da kamfanin Netay Agro-Tech a Najeriya domin bunƙasa noman dabino a jihar. 

Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi bakuncin wata tawaga daga ɗaya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya waɗanda suka ƙware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki.

Jagoran tawagar, Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf, ya bayyana kudirin kungiyar na kawo sabbin dabarun noma na zamani jihar Jigawa.

Ya ce, “Muna son tabbatar da samar da dabino a kowane lokaci a shekara ba iya kaka ba. Hadin gwiwarmu za ta kunshi horar da manoma da kuma karfafa matasa.

“Muna kuma son mu gabatar da wasu nau’in dabino mafi daraja da riba Wanda ake samar wa a kasar Saudiyya da za a noma a Jigawa.

“Wannan hadin gwiwa ba wai kawai zai kara yawan dabino da ake nomawa a Jigawa ba ne, zai inganta dabinon da ake samar wa, wanda hakan zai sa jihar ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da Afrika,”

A nasa jawabin Gwamna Namadi ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya yi daidai da ƙudurinsa na bunƙasa noma na jihar.

Ya ce “muna maraba da ku a jihar Jigawa kuma mun yaba da sha’awar ku na yin aiki da mu.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na samar da kayan aiki da suka dace domin tabbatar da gudanar da noman cikin nasara tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za a samu gagarumin alfanu da kuma matsayin jihar Jigawa a matsayin wadda ke kan gaba a harkar dabino a duniya.

Abubakar Musa-Bamai na kamfanin Netay Agro-Tech, ya ce an riga an yi nisa a wasu ayyuka, waɗanda suka haɗa da nazarin kasa da tuntubɓar juna da cibiyoyin bincike.

Ya ce, an gano cewa za a iya noma nau’in dabino guda hudu da ake nema ruwa a jallo na Mejdool (Meju), Barhi (Bari), Sukkari (Sukari) da Ajwa.

A yayin ziyarar, tawagar Saudiyya tare da wakilai daga Netay Agro-Tech sun zagaya wurare daban-daban a fadin jihar. Kamar yadda kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?