Home » Kungiyar Editocin Najeriya  Ta Karrama Kwamishinan Yaɗa Labaran JIhar Kano 

Kungiyar Editocin Najeriya  Ta Karrama Kwamishinan Yaɗa Labaran JIhar Kano 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Kungiyar Editocin Najeriya NGE ta karrama Kwamishinan yaɗa labaran Jihar Kano Kuma tsohon Shugaban Kungiyar, Baba Halilu Ɗantiye. . 

Baba Halilu Dantiye ya samu wannan lambar yabo ne  a wajen liyafar cin abinci da gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri ya shiryawa ƙungiyar a ƙarshen taron ta na bana da aka gudanar a jihar.

Da yake jawabi a wajen liyafar, Shugaban ƙungiyar Editocin Eze Anaba ya ce Baba Dantiye ya cancanci wannan karramawa sakamakon shi ya ƙirƙiro da taron a karo na farko a shekara ta 2004.

Eze Anaba ya ce nasarorin da aka samu sun ta’allaƙa ne da kyayyawan tsinkaye da wannan gwarzon Shugaba ya yi yayin shugabancin ƙungiyar.

Hakazalika ya yaba wa Gwamnatin Jihar Bayelsa da ta baiwa ɗan kungiyar ta Fred Fagbo Shugabancin Gidan Radio Da Talabijin da gidan Jaridar Jihar.

Da yake jawabi yayin miƙa lambar karramawa ga Tsohon Shugaban, Gwamnan Jihar Bayelsa Sanata Douye Diri ya yaba wa ƙungiyar domin zabar jihar sa don yin babban taron na bana. 

Gwamna Sanata Diri Ya bayyana ƙoƙarin Gwamnatin sa na ciyar da ma’aikata gaba musamman jajirtattu da masu kishin cigaban tattalin arziƙin Jihar.

Ya kluma koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da cigaban al’ummar Jihar inda ta Kasa gyara musu wutar lantarki da ƴan ta’adda suka jefa su cikin duhu na tsawon watanni 3.

Mahalarta Taron sun bayyana gamsuwa da irin ci gaba da aka samu a Jihar ƙarkashin gwamna Diri.

Kaɗan daga cikin ayyukan da Editocin suka ganewa idanunsu, akwai gyaran Gidan Radio Da Talabijin na Nijer Delta Corporation, rukunin gidajen Kwamishinoni da ‘Yan Majalisa, da aikin Gina tituna da gadoji Alan kogin Nun wanda zai laƙume biliyoyin kuɗi.

An kammala taron ne da rantsar da sababbin ƴaƴan kungiyar 12 ciki har da shugabar gidan Talabijin na Abubakar Rimi Hauwa Isa Ibrahim da Mataimakiya darakta a yaɗa Labarai Halima Ahmad Ishaq.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?