NOA Ta Bukaci Masana’antar Fina-finai Ta Inganta Dabi’u Da Martaba Nijeriya.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci kungiyar masu shirya fina-finai data yi amfani da masana’antar wajen inganta dabi’u da al’adu da martaba Nijeriya.

Darktan Janar na hukumar, Mallam Lanre Issa-onilu, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi mambobin kungiyar reshen babban birnin tarayya Abuja.

Mallam Lanre, ya ce fina-finai suna da tasiri sosai wajen chanja tunani da kuma hada kan kasa , inda ya shaidawa tawagar cewa hukumar NOA na shirin hada kai da masana’antar fina-finan don wayar da kan jama’a cikin shirye-shiryensu na film.

Shugaban masu shirya fina-finai reshen babban birnin tarayya Abuja, Desmond Utomwen, ya yabawa hukumar kan kokarin da take yin a wayar da kan jama’a da inganta dabi’u tare da yin alkawarin hada kai da hukumar don fito da fina-finai da za su wayar da kan yan kasa da suka shafi inganta dabi’u da kishin kasa.

Post masu alaƙa

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi zuwa shekarar 2060.

Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu

Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe