Jagoran jam’iyyar NNPP, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta wani rahoto na jaridar Premium Times da ke cewa ya goyi bayan shirin sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Wannan na cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Saifullahi Hassan, ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce rahoton ba shi da tushe ballantana makama, inda ta jaddada cewa babu wani lokaci da Kwankwaso ya amince ko ya nuna goyon baya ga duk wani yunƙuri na sauya sheƙar Gwamnan Kano daga NNPP zuwa APC.
Sanarwar ta ƙara da cewa Kwankwaso na nan daram kan manufofi da akidun NNPP, yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar zama gwamna a karkashin jam’iyyar, kuma har yanzu mamba ne a cikinta.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Kwankwason ya umarci magoya bayansa da ke da muƙamai su amsa kiran gwamnati.

