Wike Ya Gindaya Wa PDP Sababbin Sharuɗa

Wasu ƴan jam’iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja, inda suka fitar da wasu sharuɗa da suka ce a cika kafin babban taron jam’iyyar, wanda za a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban bana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

A wata sanarwa da suka fitar a yau Talata, mutanen waɗanda suka kira kansu da suna Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of the PDP, sun ce sun amince da tsarin rabon muƙaman jam’iyyar, amma suka ce ba za su aminta da ƙara rarraba muƙaman ba zuwa jihohi, bayan rabon a tsakanin yankunan.

Haka kuma sun ce duk da sun amince a bar shugabancin jam’iyyar a arewa, suna so ne shugaban ya fito daga yankin arewa ta tsakiya.

Sauran sharuɗan su ne:

  • Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar a Ebonyi da Anambra
  • Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar na Kudo maso Gabas
  • Amincewa da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calaba
  • Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomin a Ekiti ba tare da ɓata lokaci ba

Sanarwar ta ƙara da cewa idan har aka yi adalci, jam’iyyar PDP za ta magance matsalolin da take fuskanta sannan ta dawo da ƙarfinta.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya