NDLEA Ta Kama Iyali Guda Bisa Zargin afarar Kwayoyi

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama wani ɗankasuwa da matarsa da ‘ya’yansa mata biyu da zargin safarar ƙwaya.

National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce ta kama mutumin mai suna Ajah Johnson Uchenna ne bayan gudanar da bincike da kuma wasun ayyuka kafin hakan.

Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya faɗa cikin wata sanarwa cewa ‘yansandan farin kaya ne suka fara kama mutanen tun ranar 13 ga watan Yuni, amma da bincike ya tsananta sai aka sake kai samame gidansu ranar 1 ga watan Yuli a jihar Legas.

An kama su ne da ƙunshin ƙwayar skunk mai nauyin 277.5kg tun da farko, kafin a sake gano wata mai nauyin 231kg, inda daga nan ne aka mayar da su hannun NDLEA.

Post masu alaƙa

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.