Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da ƙudirin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka gabatar na sanya jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jerin waɗanda za a ƙaƙaba wa takunkumi.
Wasu ’yan majalisar Amurka sun gabatar da ƙudirin neman hana Kwankwaso biza tare da ƙwace kadarorinsa, bisa zargin sa da hannu wajen take ’yancin addini.
Da yake mayar da martani, Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP na Ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce Kwankwaso bai aikata wani laifi ba, don haka bai kamata a sanya shi cikin waɗanda ake zargi ba.
“Muna kallon wannan mataki a matsayin wani shiri da aka ƙulla kan mutum marar laifi wanda ba shi da alaƙa da tsattsauran ra’ayi a Najeriya.
“Tarihinsa a bayyane yake, don haka ya kamata a bincika sosai kafin a yanke hukunci,” in ji Johnson.
Jam’iyyar ta kuma tambayi dalilin da ya sa aka ware Kwankwaso shi kaɗai kan batun aiwatar da dokar Shari’ar Musulunci a Kano.
Jami’yyar ta ce ba Kwankwaso ne kaɗai ya aiwatar da dokar ba har ma da wasu jihohin Arewa, don haka ta nemi a yi adalci.
NNPP ta kuma tuna cewa Kwankwaso ya taɓa yin martani lokacin da Amurka ta sake ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matsala ta musamman.
Ya yi gargaɗin kada a ɗauki matsalolin tsaro na ƙasar a matsayin abin da ya shafi addini ɗaya face ’yan ta’adda da masu aikata laifi na kashe kowa da kowa.
“Waɗannan su ne hujjojin da muke ganin ya kamata su jagoranci Majalisar Dokokin Amurka wajen yin cikakken bincike kan gaskiyar lamarin.
“Yana da kyau a yi wa jagoranmu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, adalci tare da wanke sunansa daga wannan zargi,” in ji jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa a lokacin da yake gwamnan Kano, Kwankwaso ya yaƙi Boko Haram tare da kyautata alaƙa da shugabannin Kiristoci.
Ta kuma ce a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya tsaya takara tare da Kirista a matsayin mataimakinsa, abin da ta ce ya nuna kishinsa ga haɗin kan ƙasa.