PDP Ta Tabbatar Da Damagum A Matsayin Shugabanta Na Nasa

Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.

Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.

Post masu alaƙa

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi