PDP Ta Miƙa Wa Kudancin Najeriya Takarar Shugaban Kasa A 2027

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja.

A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027.

A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.

Damagum wanda ya shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar a yanzu ya zama shugaba mai cikakken iko gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a gudanar a ranakun 15 a 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

A watan Maris ɗin 2023, PDP ta naɗa Damagum a matsayin shugaban riƙo, bayan dakatar da shugabanta na wancan lokacin, Sanata Iyorchia Ayu.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto