An rufe jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina bayan rashin jituwa da ta taso tsakanin hukumomin jami’ar da gwamnatin jihar.
Dr. Murtala Abdullahi Ƙwara, wanda shi ne shugaban ƙungiyoyin ma’aikata na jami’ar ya tabbatar wa BBC cewa an rufe jami’ar ne ranar Litinin bayan gazawar gwamnatin na cika wasu sharuɗɗa biyar da ma’aikatan jami’ar ta gindaya.
Ƙwara ya ce yajin aikin ya haɗa da dukkanin ƙungiyoyin ma’aikatan jami’ar guda huɗu, waɗanda suka haɗa da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da ta manyan ma’aikatan jami’a (SSANU), da ta matsakaitan ma’aikata da kuma ta masu aiki a ɗakunan bincike.
Ya bayyana cewa “wannan ne karo na farko da aka taɓa kulle jami’ar baki ɗaya sanadiyyar rashin aiki, kasancewar kowace ƙungiya kuma kowane ma’aikaci ya ƙaurace wa aiki.”
Murtala ya ce buƙatun da suka gabatar wa gwamnati sun haɗa da daidaita albashin ma’aikatan jami’ar da na jami’o’in tarayya, da batun bai wa jami’a ƴancin ci gaba da tafiyar da shafin intanet na jami’ar, sai kuma batun fansho da kuma na amfani da asusun bai-ɗaya.