Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci rundunar sojin Najeriya da su kasance masu ladabi, haɗin kai da kuma martaba dimokuraɗiyya.
Ya bayyana sojoji a matsayin ginshiƙin wajen haɗin kan ƙasa da kuma kare dimokuradiyyar Najeriya.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa sojoji domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar nan.
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, a lokacin bikin Tunawa da ’Yan Mazan Jiya na shekarar 2026 tare da bikin karrama wasu jami’ai.
Ya ce a matsayinsa na Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya, yana kira ga dakarun da su kasance masu biyayya, ladabi, aminci da haɗin kai.
Ya ƙara da cewa a ƙasa mai al’ummomi da yawa kamar Najeriya, sojoji su ne ginshiƙin ƙarfin haɗin kanta.
Shugaban ya buƙaci sojoji da su kasance masu biyayya ga Kundin Tsarin Mulki da dimokuraɗiyya, tare da buƙatar kare iyakokin ƙasar.
Tinubu ya ce walwalar sojoji tana da alaƙa kai-tsaye da tsaron ƙasa.