Shugaba Bola Tinubu Lafiyarsa Kalau – Gwamna Soludo

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi.

A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba.

Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya ce Tinubu na na kalau.

“Shugaban Kasa na nan kalau, kuma cikin koshin lafiya yana kuma ci gaba da ganawa da jama’a, kuma ni ma na ji dadin tattaunawa da shi,” in ji Gwamnan.

Baya ga Gwamna Soludon, shi ma takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada da kuma Ministan Kudi Wale Edun, su ma sun je fadar don ganawa da Tinubu a ranar ta Litinin.

Gwamnan Soludo dai wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, ya yi kira ga jama’a da su yi gangamin mara wa Tinubu baya, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran bunkasa Dimokuradiyya da habaka tattalin arzikin Najeriya.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC