Zaben Cike Gurbi: Jam’iyun Siyasa Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Kano

Rundunar yan sandan sandan jihar Kano, ta gudanar da taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyun siyasa, gabanin zabukan cike gurbi, da za a gudanar a kananan hukumomin, Ghari/Tsanyawa da kuma Bagwai/ Shanono, a majalissar dokokin jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori , ne ya jagoranci zaman tattaunawar da shugabannin jam’iyun da kuma yan takararsu, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano.
Za a gudanar da zaben a ranar Asabar 16 ga watan augustan 2025.
A zaman tattaunawar duka jam’iyun siyasar, sun rattaba hannu akan takaddar yarjejeniyar zaman lafiya, lokacin zaben da kuma bayansa.

Kwamishinan yan sandan ya bada tabbacin cewa za a jibge isassun jami’an tsaro, kuma ya gargadi dukkan jam’iyun su yi yakin neman zabensu bisa dokar zabuka , don wanzar da zaman lafiya kamar yadda suka yi alkawari.
Sai dai ya ce duk wanda aka samu ya haifar da Rashin zaman lafiya doka zata yi aiki akansa ba tare da jin kunya ko tsoro ba.
A karshe ya yi fatan jam’iyun za su ba wa hukumomin tsaro hadin kai don ci gaba da samar da zaman lafiya mai dorewa yayin gudanar da zabukan dama bayansa.
Don sanar da yan sanda wani abu da ba a amince dashi ba, ko neman taimakon gaggawa a kira : 08032419754, 08123821575, 09029292926.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda