Shugaban DSS ya kai wa Tinubu rahoto kan matsalar tsaro

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Najeriya ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tnubu rahoton halin da ake ciki game da sace-sacen ɗalibai da ‘yanbindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja da ke arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu, ya fitar ta ce shugaban DSS, Tosin Adeola Ajayi, ya gana da Tinubu ne a jiya Juma’a da dare.

A ranar Litinin ne ‘yanbindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga wata sakandare a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma.

Sai kuma ranar Juma’a wasu ‘yanbindiga suka sace ɗalibai fiye da 300 da malamansu a wata sakandaren da ke Papiri a cikin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.

Tuni Tinnubu ya soke balaguronsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu saboda halin matsalar tsaron, kuma ya tura Ministan Tsaro Abubakar Badaru Neja, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tafi Kebbi.

Post masu alaƙa

Da buƙatar samar da takin zamani ga manoman Najeriya – MDD

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kammala tantance masu neman shiga aikin ɗan sanda

Ƴan sanda sun tsaurara tsaro a cibiyoyin JAMB jihar a Jigawa