Bola Tinubu

Tinubu ya isa Abu Dhabi don halartar taron makamashi

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar wani taron makon makamashi. Cikin wata sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Shugaba Tinubu ya samu tarba daga ministan harkokin wajen ƙasar UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, da jakadan UAE a Najeriya a ƙasar, Salem […]

Read more

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin ƙarfafa dakarun ƙasar

Gwamnatin Najeriya ta alƙawarta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar domin magance matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar. Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin taron addu’o’i na musamman ga dakarun tsaron ƙasar da aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar. Shettima ya […]

Read more

Tinubu Ya Miƙa Sunan Dambazau A Matsayin Ambasada

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura ƙarin sunan mutum 4 ɗoriya a kan waɗanda aka fitar a baya zuwa ga majalisar dattawa domin a tantance su a matsayin jakadun ƙasar da za a tura ƙasashen waje. Mutum huɗu da Tinubu ya tura su ne: Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon shugaban riƙon-ƙwarya na jihar Rivers da tsohon […]

Read more

Tinubu ya rantsar da Chris Musa ministan tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan amincewar majalisar dattawa. An yi bikin rantsar da tsohon babban hafsan tsaron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis, kwana ɗaya bayan ‘yanmajalisar dattawan sun shafe kusan awa biyar suna yi masa tambayoyi yayin tantance […]

Read more

Gwamnan Abia ya ziyarci Tinubu a Villa

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Shugaba Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja. Duk da cewa babu cikakken bayani game da ziyarar, wasu a ƙasar na ganin ba ta rasa nasaba da batun shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biafra, Nnamdi Kanu da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da rai cikin watan da ya […]

Read more