APC Ta Lashe Zaɓukan Cike Gurbi A jihar Kaduna

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe duka zaɓukan cike gurbi uku da aka gudanar a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar, kamar yadda hukumar zaɓe ta Inec ta sanar.

Sakamakon da aka gudanar a mazaɓar majalisar tarayya ta Chikun/Kajuru ya nuna cewa Felix Bagudu na APC ɗin ya samu ƙuri’a 34,580 kuma ya doke na PDP da ya zo na biyu da ƙuri’a 11,491.

Kazalika, APC ta yi nasarar cin zaɓen ‘yanmajalisar jiha na mazaɓun Zaria/Kewaye da kuma Basawa.

Baturen zaɓe na Zaria Kewaye Balarabe Abdullahi ya sanar cewa ɗantakarar APC Haruna Ihamo ne ya cinye da ƙuri’a 26,613, yayin da abokin hamayya na SDP Nuhu Sada ya samu 5,721.

A zaɓen Basawa kuma, baturen zaɓe Farfesa Nasiru Rabiu ya ce APC ta samu ƙuri’a 10,926 kuma ta doke PDP mai 5,499.

Da ma APC ce ke mulkin jihar ta Kaduna bayan ɗantakararta Uba Sani ya lashe zaɓen gwamna na watan Maris ɗin 2023.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda