Nigeria

Yadda Aka Kama Yan Dabar Siyasa 288 A Kano

  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Ya bayyana cewa an yi […]

Read more

An Sake Ceto Matafiya 10 Da Aka Sace A Kogi

Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi. Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata […]

Read more

Sojojin Najeriya Sun Musanta Miƙa Wuyan Bello Turji

Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan wanda ya yi ƙaurin suna, Bello Turji ya miƙa wuya ga sojojin ƙasar. Daraktan yaɗa labarai da aikace-aikacen shelkwatar tsaron, Manjo-Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhamis. “Maganar ita ce Bello Turji bai […]

Read more

Za A Gina Layin Dogo Mai Amfani Da Lantarki A Kano

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da titin dogo domin sufurin jirgin ƙasa a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin ƙasar, wanda zai laƙume naira triliyan 1 da rabi, a kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana. Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito ɗan majalisar yana bayyana hakan ne a […]

Read more

Ƴan sanda Sun Saki Omoyele Sowore

Rundunar ƴansandan Najeriya ta saki ɗangwagwarmaya, Omoyele Sowore bayan kiraye-kirayen da aka yi na buƙatar a sake shi. Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasan ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya alaƙanta sakin nasa da nasarar kiraye-kiran sakin nasa da aka yi. Ya rubuta cewa, “Ƴansandan Najeriya sun amsa buƙatar ƴan gwagwarmaya. Yanzu haka […]

Read more

Matatar Dangote Ta Janye Karar Da Ta Kai NNPCL Kotu

Matatar man Dangote ta janye ƙarar da ta shigar a gaban kotu kan hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA da kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, da kuma wasu kamfanonin mai guda biyar. Ƙarar da aka shigar ta nemi waɗanda ake ƙara da su biya diyyar naira […]

Read more

NIMC Ta Gargadi Yan Najeriya Kan Bayar Da Bayanansu

Hukumar Kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC) ta bayyana damuwarta kan yadda wasu ƴan ƙsar ke sayar da bayanansu, ciki har da lambar shaidar ɗan kasa (NIN), domin samun kuɗi. Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fitar cewa wasu mutasa na biyan mutane naira […]

Read more