Shugaba Tinubu ya miƙa ragamar shugabancin Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ga Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio.
Yanzu shugaba Saliyo, Julius Maada Bio ne zai cigaba da jagorancin Ƙungiyar ta ECOWAS.
Yayin jawabin kama aiki, sabon shugaban na ECOWAS ya ce, “Dole mu sake fasalin ECOWAS ta yadda za ta zama mai gaskiya, inganci da amsa buƙatun al’ummarta,”
- Tinubu Na Bani Dariya In Yana Maganar Dimokuradiyya-Sule Lamido
- Yan Sanda Sun Gano Sauran Abubuwan Fashewa 7 A Kano
Shugaba Tinubu ya yi fama da matsaloli da yawa yayin shugabancin ƙungiyar, inda a lokacin shugabancinsa ne ƙasar Nijar da Burkina Faso da Mali suka fice daga ƙungiyar.
An kafa ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka ne a ranar 28 ga watan Mayu a shekarar 1975.