Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai jagoranci taron addu’o’i na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar ta ce taron – wanda za a gudanar da misalin ƙarfe biyar na maraice agogon ƙasar – zai samu halartar ministocin gwamnatin ƙasar.
Taron zai kuma samu halartar shugabannin majalisun dokoki da wakilai daga fannin shari’ar ƙasar.
Taron addu’ar na zuwa ne bayan addu’ar uku da rasuwar tsohon shugaban da aka gudanar a Daura a gaban tawagar wakilan gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da taron addu’o’i na musamman ranar Juma’a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja