Babban Sifeton ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya amince da aika jami’an ƴansanda 45,000 domin bayar da tsaro a lokacin zaɓen gwamnan jihar Anambra da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamban 2025.
Egbetokun – wanda kwamishinan ƴansanda mai lura da dakarun kai ɗaukin gaggawa – ya bayyana hakan ne ranar Talata a lokacin wata ganawa da kwamitin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da aka gudanar a shalkwatar hukumar zaɓen ƙasar da ke Abuja.
Babban Sifeton ƴansandan ya ce jami’an da za a tura za su tabbatar da tsaro a kafin zaɓen da lokacin zaɓen da ma bayan zaɓen.
Ya ƙara da cewa za a fara tura jami’an ne tun daga ranar 1 ga watan Nuwamba domin kawar da duk wata barazana ga zaɓen.
Egbetokun ya kuma ce baya ga jami’an ƴansanda akwai sauran hukumomin tsaro da za su taka rawa a zaɓukan da suka haɗa da na farin kaya, DSS da rundunar tsaron fararen hula da sibil difens da sojoji.