Rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da matashinan mai suna, Ibrahim Abubakar, mai shekaru 19 , wanda ake zargin da yunkurin kashe kansa bayan ya hau kan wani allon talla (bill board) dake kusa da Ado Bayero kan titin zuwa Maiduguri Road a jihar.
Cikin wani sako da wallafa a shafinsa na facebook kakakin rundunar yan sandan jihar , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an gurfanar da matashin ne a gaban kotun magistire mail amba 5 dake zaman ta a unguwar Gyadi-gydi dake Kano.
SP Kiyawa ya ce ana tuhumar matashin da yunkurin kashe kansa, ta hanyar yin ikirarin zai fado daga saman Allon tallan matukar wani dan Tiktok da ake kira Abdul BK ba zai zo ba.
Tun a ranar litinin din data gaba ne rundunar yan sandan ta samu nasarar sauko da matashin tare gwiwar ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Kano.
Ganduje Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Jam’iyyar APC
A wata sanarwar mukaddashin kakakin yan sandan Kano ya fitar DSP Hussaini Abdullahi, ya ce sakamakon, a wannin da matashin ya shafe a saman allon , ya wahala sosai saboda yunwar da yake ji, kuma bayan sauko dashi aka garzaya dashi asibitin yan sanda dake unguwar Bompai don samun kulawar gaggawa.
Kuma wanda yake ikirarin sai ya zo sannan zai sakko ya zo wajen wato Abdul Bk.
Daman Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan faruwar lamarin , kuma ya gargadi jama’a da su guji irin wannan danyen aiki domin duk wanda aka samu za a hukunta shi.