Za A Yi Wa Aminu Ɗantata Salatul Ga’ib A Kano

Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Alhasan Ɗantata rasuwa.

Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu ya rasu yana da ’ya’ya bakwai da jikoki da dama.

Babban sakatarensa, Mustapha Abdullahi Junaid, ne ya sanar da rasuwar a safiyar Asabar.

Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)

Alhaji Aminu Ɗantata shi ne mai kamfanin mai na Express Petroleum & Gas, kuma a matsayin uba yake ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote.

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta sanar da cewa za a yi masa sallar a Kano ba tare da gawarsa ba (Salatul Ga’ib) da misalin ƙarfe biyu na rana.

Shugaban Majalisar Malamai, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa za a gudanar da sallar a masallacin Aliyu Bn Abi Ɗalib, da ke Dangi a cikin birnin Kano.

Ya bayyana cewa, an yanke shawarar yin Salatul Ganin ne saboda attajirin ya rasu ne a ƙasar waje, inda za a yi masa sutura a Dubai.

Tarihin Aminu Ɗantata

Alhaji Aminu Dantata ya kasance  wani babban jigo a harkokin kasuwanci, addini, da tallafawa al’umma a Najeriya.

Kasuwancinsa ya shafi fannoni daban-daban, ciki har da gini, masana’antu, banki, noma, da kuma mai da iskar gas.

Ƙarƙashin jagorancinsa, harkokin kasuwancin Ɗantata ta bunƙasa kuma ta zama ginshiƙi ga ci gaban kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya.

Ya kuma riƙe muƙamai da dama a bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, inda ya jagoranci ’yan kasuwa, masu tsara manufofi, da shugabannin al’umma.

Duk da dimbin dukiyarsa da tasirinsa, Ɗantata ya kasance mai mutunta jama’a da tawali’u da jajircewarsa wajen hidimta wa ci-gaban al’umma.

Ayyukansa na tallafawa al’umma sun haɗa da kafa da kuma ba da kuɗin makarantu, masallatai, cibiyoyin kiwon lafiya, gidajen marayu, da tallafawa gwauraye da marasa galihu a duk faɗin Najeriya, musamman a yankin Arewa.

Gidauniyarsa ta ƙashin ƙansa da gudummawar da ya bayar a ɓoye sun shafi rayuwar mutane marasa adadi tsawon shekaru da dama.

Rasuwar Alhaji Dantata ta jawo dimbin sakonni na jaje daga shugabannin kasuwanci, jami’an siyasa, malamai, da kuma talakawa ‘yan Najeriya waɗanda suka amfana daga karamcinsa da jagorancinsa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda