‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Daba 24 Da Muggan Makamai A Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 24 da ake zargin ‘yan daba ne tare da ƙwato muggan makamai a yayin wani sumame da ta gudanar a tun daga ranakun 13 zuwa 16 ga Disamba, 2024.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an gudanar da aikin ne da nufin magance tashe-tashen hankula da fadace-fadace tsakanin matasa a yankunan Kofar Mata, Yakasai, Zango anguwar Zage, da kewaye.

Kiyawa ya ce, an tura ‘yan sandan ne bisa umarnin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun domin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro.

Baya ga haka, rundunar ‘yan sandan ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da suka hada da Hakimai, ’yan banga, dattijai, da ’yan kasuwa.

An kuma gudanar da gangamin wayar da kan jama’a ta gidajen rediyo da talabijin da kafofin sada zumunta da fata inganta hadin kan al’umma wajen tabbatar da tsaro.

 

 

Related posts

Ba Daidai Ba Ne Tinubu Ya Ci Gaba Da Ciyo Bashi Duk Da Cire Tallafin Mai – Sanusi

Yan Sanda Dubu 45,000 Ne Za Su Kula Da Zaben Jihar Anambra

Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka