Zainab, diyar shahararren ɗan siyasar nan Buba Galadima ta ce duk da cewa ita ‘yar jam’iyyar APC ce, amma abu mafi hatsari da mutum zai yi a Najeriya shine zama ɗan APC, saboda a halin da ake ciki yanzu.
Zainab Buba Galadima ta ce, ba ta faɗi haka domin tana son barin jam’iyyar ba, sai dai saboda halin da ƙasar nan ke ciki.
Yayin wata tattaunawa Zainab ta ce an taba fasa mata gilashin mota saboda ita ‘yar APC ce kuma ‘yan Najeriya suna ganin jam’iyyar bata tsinana musu komai ba.
- Kotu Ta Ce ‘Yan Sanda Su Kama Masu Sayar Da Makamai A Kano
- Kotu Ta Umarci A mayar Da Sanata Natasha Majalisa
Zainab ta kuma ce su kansu ‘ya’yan APC suna cikin wani hali, ta bada labarin cewa an taɓa shirya taron jam’iyyar a Abuja amma mutum guda ta gani da hula mai tambarin su.
Dangane da yadda take kallon halin da kasa ce ciki, Zainab ta ce “Gaskiya APC sun bani kunya, ana cikin wani hali a Najeriya”.