Zan Iya Rantsuwa Da Alƙur’ani Ban Saci kuɗin Gwamnati Ba-Nasiru El’rufa’i

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufa’ ya bayyana cewa a shirye ya ke ya rantse da Al’ƙur’ani akan bai saci ko sisi daga asusun gwamnatin Jihar Kaduna ba.

El’rufai ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da ‘ƴan jarida

El’rufa’i wanda shine gwamnan jihar kaduna daga  shekarar 2015 zuwa 2023 ya bayyana cewa bai shiga gwamnati dan ya azurta kansa ba, sai dai domin ya hidimtawa al’umma.

A baya-bayan nan ne dai majalisar jihar Kaduna ta zargi El-rufa’I da karkatar da tsabar kudi har Naira Biliyan ɗari huɗu da arba’in da uku a lokacin da yake gwamnan jihar.

To sai dai El’rufa’I da muƙarraban gwamnatin sa na wancan lokacin sun musanta wannan zargi, inda suka bayyana shi amatsayin zance mara tushe balle makama.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa da Zarar ya kammala karatunsa zai dawo fagen siyaysa domin cigaba da hidimtawa al’umma.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere