CP Bakori Ya Jagoranci Karawa Wasu Yan Sanda 1,020 Girma A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, bisa jagorancin kwamishinan ta CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta karawa jami’anta biyu girma , a matakai dabam-daban. An gudanar da taron Karin girman a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda dake unguwar Bompai Kano. Kwamishinan yan sandan, ya bukaci yan sandan da suka sami karin girman, y ace wannan […]

Read more

Ma’aikatan Jinya Sun Dakatar Da Yajin Aiki A Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce ma’aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi. Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma’a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin […]

Read more

Yan Najeriya Miliyan 34 Na Cikin Barazanar Yunwa

Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a […]

Read more

Rundunar Sojin Ruwan Najeriya Za Ta Kafa Sansani A Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a garin Yauri na jihar Kebbi a wani mataki na bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa. Matakin na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kebbi a ranar Alhamis. Tawagar ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda […]

Read more

Gwamnatin Tinubu Ta Mayar Da Arewa Saniyar ware – ACF

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a yankin. Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu […]

Read more

Kungiyar Malaman Jami’ar jihar Yobe Ta Janye Yajin Aiki

Ƙungiyar malaman jami’a reshen jami’ar jihar Yobe sun sanar da janye yajin aiki da suka shiga ranar 11 ga watan Yulin, 2025. Shugaban malaman jami’ar, Ahmed Karange, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar ta Yobe, inda ta yi alkawarin biyan sauran buƙatu da malaman ke nema. “Bayan cimma yarjejeniyar, shugaban malaman jami’ar […]

Read more